Akalla mutane 20 ne suka rasa rayukansu ciki har da wasu jami’an soji biyu a lokacin da wasu da ake zargin mayakan ISWAP ne da sojojin Najeriya suka yi arangama a wani sansanin soji da ke Rann, hedikwatar karamar hukumar Kala Balge a jihar Borno ranar Juma’a.
Majiyoyin tsaro sun ce lamarin ya afku ne da misalin karfe 1:30 na sanyin safiyar Juma’a a garin Rann mai iyaka da kasar Kamaru.
Kungiyar ta bukaci masu ruwa da tsaki da su yafe, su amince da mika wuya daga kungiyar Boko Haram.
An gano cewa sojojin sun kashe fiye da goma na haramtacciyar kungiyar tare da lalata motocin da suke gudanar da ayyukansu.
Wata majiyar tsaro ta bayyana cewa maharan sun hau kan wasu motocin alfarma sanye da bindigu na kakkabo jiragen sama domin kutsawa cikin garin inda suka yi artabu da sojoji.
“Abin takaici ne yadda wani kaftin, Laftanar da sojoji shida suka rasa rayukansu tare da mayakan ISWAP kusan 16 a wannan kazamin yakin.”
A halin da ake ciki kuma, majiya mai tushe ta ce an kai hari a Malam Fatori, hedikwatar karamar hukumar Abadam ta jihar Borno.
Garin da ke kan iyaka da Jamhuriyar Nijar, mayakan Boko Haram sun kai hari da dama a yankin.
A baya-bayan nan ma, ‘yan kungiyar ISWAP masu ballewa daga kasar sun yi wa garin kawanya inda suka nufi jami’an tsaron Najeriya.
Ba a dai bayyana abin da ya faru a daren jiya a garin ba amma daya daga cikin majiyarmu ta ce an samu rashin zaman lafiya da kuma tashin hankali a yankin
Gwamnatin jihar Borno ta mayar da daruruwan mutanen yankin da suka zama ‘yan gudun hijira a wasu wurare zuwa gidajensu.
Comments 1