Hukumomin kasar Saudiyya sun kame wasu yan Najeriya da dama wadanda suka je aikin Umra a watan Ramadan din da ya gabata.
Wata sanarwa daga mahukuntan kasar Saudiyyar ta bayyana cewa sun kame mutanen ne, sakamakon yadda suka dinga daga Fastar siyasa a dakin Ka’aba.
”Maimakon matasan su koma aiwatar da addu’a ga kasar su sai suka buge da daga hotunan yan siyasa,” cewar sanarwar.
Wannan na zuwa ne adaidai lokacin da yan Najeriya ke ci gaba da Allah wadai da yadda wasu mutane suka dinga Daga Fastar Dan Takarar Shugaban Kasa Bola Tinubu.
Hakan dai ya bata ran da dama cikin al’ummar musulmi, wanda suke ta kiraye kirayen ganin mahukunta sun dauki matakin da ya kamata.
Mutanen da aka kama dai sun kai akalla Mutum 30.
A halin da ake ciki dai majiyar daga Saudiya ta bayyana cewa wadanda aka kama suna hannun mahukunta kasar, karkashin kulawar askarawa domin gurfanar dasu gaban kotu tare da yanke masu hukunci dai-dai da abinda suka aikata.