Jami’an rundunar soji na Operation Safe Haven sun dakile wunkurin harin masu Garkuwa da mutane har sau biyu a karamar hukumar Jema’a dake jihar Kaduna.
Kwamishinan kula da harkokin cikin gida da al’amuran tsaro Samuel Aruwan ne ya tabbatar da wannan nasarar a yau Asabar, Inda ya ce, lokacin samamen, rundunar ta kuma yi nasarar ceto Mutane shida, daga cikin wadanda yan bindigan su ka yi garkuwa da su.
Ya ce, “Kamar yadda muka sami rahotanni, lamarin ya faru ne a kan hanyar Badde zuwa Ungwan Ayaba da Keffi, inda yan bindigan su kayi yunkurin garkuwa da direbobin motar haya, dake kokarin shiga garin Abuja.”
KARANTA WANNAN LABARIN: Mai shakkar auren Yar fim, Daman ba dagaske ya ke ba, inji Fati Yola
“Jami’an sojin sun amsa kiran direbobin motar cikin gaggawa, inda suka Isa wurin da lamarin ke faru, kuma su ka yi nasarar kubutar da Fasinjoji 5 daga cikin wadanda yan bindigan su ka yi garkuwa da su”
“A wani makamancin irin wannan lamarin kuwa, jami’an sojin sun yi nasarar kubutar da Mutum guda, a kan hanyar Fanock zuwa Kyayya da Keffi na karamar hukumar Jema’a, bayan Yan bindigan sun yi garkuwa da shi, a cikin motar shi” kamar yadda ya bayyana.
Kazalika Samuel Aruwan ya ce, ” An ceto mutumin ne dauke da rauni a kafar sa, Kuma an kai shi asibiti, domin duba lafiyar shi.” inji shi.