• Sojojin dake bakin aiki a kan bababn hanyar Maiduguri zuwa Dammaturu me su ka dakile harin da yan bindiga su kayi yunkurin kai musu.
• Lamarin ya afku ne a garin Auno dake kan hanyar.
• A watan Afurilu irin wannan lamarin ma ya faru Wanda ya yi sanadiyar mutuwar yan bindiga da dama.
Jami’an soji dake aiki a kan babban haryar Maiduguri zuwa Dammaturu, sun dakile yunkirin kai harin wasu yan bindiga a sansanin su dake garin Auni na jihar Borno, a jiya juma’a.
Wani shaidan gani da Ido dake Auni ya ce, ” Gun-gun mahara a kan motoci hudu sun yi yunkirin kai wa sansanin sojin hari, kafin daga bisani sojin, su fattakesu.” Inji shi.
Ya ce Maharan sun boyene cikin a yarin motocin da ke fitowa daga Dammaturu, inda sukayi arangama da jami’an sojin dake kan sintiri.
Ya Kuma cigaba da cewa “Kafin fatattakan yan bindigan, wasu daga cikin sojin, sun yi kwantan bauna ne a gefen hanya, inda su kaga a yarin yan bindigan cikin kakin soji, kuma nan take su ka fara harbin su, tunda manyan su, ba su sanar da su cewa, wasu soji zasu zo wucewa ba.” In jishi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sojoji sun kashe yan bindiga a zamfara
Kazalika ya ce, ” Sojojin na shirye a kowani lokaci, domin kauce wa harin bazata.”
Idan za a iya tunawa dai, a watan Afurilu shekaran nan, yan bindiga sun yi yunkurin kai wani harin bazata a kusa da garin Mainok, wanda yayi sanadiyar mutuwar dayawa daga cikin su.
Comments 1