Rundunar Sojin Najeriya ta kama wani babban dan bindiga da Mai suna Alhaji Goma Sama’ila.
Rahotanni sun nuna cewa,an kama Samaila ne a jihar Kaduna, a daren jiya Juma’a.
Kazalika Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, Sama’ila ne ke da alhakin shirya satar shanu da dama sannan kuma ya shiga cikin Garkuwa da mutane da dama.
KARANTA WANNAN LABARIN: A yanzu Yan Fim ansha mu, mun warke, inji T.Y Shaba
Jihar Kaduna ta sha fama da manyan hare-haren garkuwa da mutane, kisan gilla, da satar shanu daga yan bindiga.
A wani labarin Kuma na daban,
Wani yaro mai kimanin shekara 17, mai suna Aliyu Zakariya dalibi a daya daga cikin makarantun sakandaren gwamnatin Kano ya fada cikin ruwa a Unguwar Kabuga dake karamar hukumar Gwale wanda kuma ya rasa ransa a sana diyyar hakan.
Tunda fari dai matashi yaron yaje wani tafkine dake unguwar Kabuga danyi kurme tare da a bokanan sa inda kuma bayan shugar sa ya kasa fitowa ya sha ruwa yayi masa yawa bisa hakanne ya fita daga cikin hayyacin sa.
Bayan faruwar al’amarin ne wani mai suna Shu’aibu Rabi’u ya kira jami’an hukumar kashe gobara ta jihar kano da misalin karfe 10:45 na safe dan kai masa agajin gaggawa kuma suka halaccin wajen cikin lokaci da karfe 11:00 na safe.
Sai dai bayan isarsu wajen sunyi kokarin tsamo yaron daga cikin kududdufin kuma sun sami nasarar kubutar dashi amma baya cikin hayyacin sa inda daga bisani aka tabbatar da ya mutu.
Jami’in hulda da jama’a na na hukumar kashe gobara ta jihar kano, Saminu Yusif Abdullahi ya tabbatar da faruwar hadarin yace sun mika gawar matshin yaro zuwa ga mahaifin sa Alhaji Zakariya dake Unguwar Dorayi danyi masa zana’iza.
Saminu yace yana kira ga iyayen yara dasu dinga sanya idanu akan shige da ficen ‘ya’yansu wajen zuwa wuri mai hadari, saboda yadda ake samun ya waitar samun masu fadawa acikin ruwa a dan takinnan.