Kwamishinan tsaron da kula da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce wasu mutane 7 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun shiga hannun dakarun rundunar ‘Operation Safe Haven’ a Mariri da ke karamar hukumar Lere a ranar Larabar da ta gabata.
Ya ce an yi zargin cewa mutanen yankin sun lallasa wani da su tare da shi kuma ake zargin dan bindiga ne.
Kwamishinan ya bayyana sunayen wadanda ake zargin Musa Adamu, Abdullahi Usman, Suleiman Hasidu, Usman Jibril, Saidu Isah, Hassan Abdulhamid da Idris Sani.
“Wata mai suna Hajiya Bilkisu, wadda ake zargi da hannu a cikin mutanen da aka kama, ta yi rashin sa’a daga wajen ‘yan unguwar sun kashe ta yayin da ta ke kokarin tserewa,” inji shi.
Bayan Shan Kakkausar Suka, Gwaman Zullum Ya Amince Da Mafi Karancin Albashi
Kwamishinan ya kara da cewa, “Hukumomin tsaro sun kai rahoto ga gwamnatin jihar Kaduna cewa an kama wasu mutane bakwai da ake zargin ‘yan bindiga ne a unguwar Mariri da ke karamar hukumar Lere.
“A cewar rahoton, an kama mutanen ne sakamakon ci gaba da tattara bayanan sirri da hukumomin tsaro ke cigaba da yi. Dakarun Operation Safe Haven sun yi aiki da sahihan bayanan sirri tare da kama wasu ‘yan kungiyar masu garkuwa da mutane.
“Gwamnatin jihar Kaduna ta lyaba da rahoton tare da yaba wa sojojin bisa matakin da suka dauka na gaggawa kan bayanan sirri da suka samu. Gwamnati ta bukaci hukumomin tsaro da su tabbatar da gudanar da cikakken bincike kan wadanda ake zargin.”