Jami’an Rundunar Operation Safe Haven sun bayyana wa Gwamnatin jihar Kaduna cewa, sun kubutar da Mutum 15 daga hannun yan bindiga a garin Jagindi dake karamar hukumar Jema’a.
Kwamishinan tsaro da kula da harkokin cikin gida Samuel Aruwan ne, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin.
Kwamishinan ya bayyana cewa, an kubutar da mutannan ne bayan da ake kokarin Kai su maboyar a motoci biyu.
A cewar shi, jami’an sojin sun isa yankin ne bayan samun wani Kiran waya na sirri, domin kubutar da wadanda yan bindigan suka sace.
KARANTA WANNAN LABARIN: Matar Tsohon Shugaban kasa ta rasu
Kazalika Aruwan ya bayyana sunayen wadanda aka kubutar kaman haka: Maisaje Pam, Samuel Peter, Ziyau Abdul, Henry Dabo, Abduljabar Auwal, Muhammad Ali, Dama Dabo and Ramatu Aminu.
Sauran sun hada da; Muhammad Sani, Abdullahi Muhammad, Bashar Garba, Abubakar Musa, Saad Yakubu, Maryam Ibrahim and Lami Bitrus.
Lokacin da ta ke jawa mukaddashiyar Gwamnan jihar Kaduna Hadiza Balarabe, ta yaba wa rundunar jami’an tsaron bisa yunkurin da suka nuna, wurin ceto wadanda aka sace.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, haryanzu jami’an sojin na kan gudanar da bincike domin Kara kubutar da wasu a yankin.
Comments 1