By Abbas Yakubu Yaura
Hukumomin tsaro sun kama wasu mutane takwas da ake zargi da hannu a sace wasu farfesoshi biyu da wasu ma’aikatan jami’ar Abuja ranar Talata.
An kama wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne a maboyarsu dake dajin Shenegwu dake yankin Gwagwalada a cikin babban birnin tarayya Abuja a yayin wani samame na hadin gwiwa da ‘yan sanda da sojoji da DSS da sauran jami’an tsaro suka gudanar a ranar Juma’a.sannan jami’an sun ceto wadanda lamarin ya rutsa dasu ba tare da sun ji rauni ba, inda aka kai su asibiti domin a duba lafiyarsu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh, tace ‘yan bindigar sun yi musayar wuta da jami’an ‘yan sanda amma abin ya ci tura.
Sanarwar mai taken, ‘Re, Satar Jami’ar Abuja, takwas na tsare, an kubutar da dukkan wadanda abin ya shafa, an gano maboyar masu laifi, “Bayan bincike da farautar masu aikata laifukan dake da hannu wajen sace ma’aikatan (mambobi) na Jami’ar Abuja.a ranar 2 ga watan Nuwamba 2021, jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya tare da hadin gwiwar sojoji, DSS da sauran jami’an tsaro a wani samame na hadin gwiwa da suka yi a safiyar Juma’a 5 ga watan Nuwamba, sun yi nasarar gano maboyar. ’yan ta’addan dake dajin Shenegwu dake unguwar Gwagwalada a babban birnin tarayya Abuja sun ceto duk wadanda aka sace ba tare da sun ji rauni ba.
“Masu aikata laifukan, da suka ga tawagar jami’an tsaro, sun yi ta harbin bindiga na kan mai uwa da wabi. Sai dai kuma karfin farmaki da bude wutar da jami’an tsaro suka yi ya kai ga kama wasu mutane takwas na gungun barayin yayin da wasu daga cikin ‘yan kungiyar suka tsere zuwa cikin dajin da kuma al’ummomin dake kusa da wajen”.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa A halin da ake ciki, rundunar ta fara gudanar da bincike kan fashewar tankar ajiye kananzir data kashe mutane biyar tare da jikkata wasu 10 a kasuwar kauyen Kubwa a ranar Juma’a.
Rundunar ‘yan sandan ta ce binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa shaguna biyu a cikin kasuwar ne gobarar ta shafa sakamakon fashewar tankar kananzir.