An ceto wasu mutane tara da aka yi garkuwa da su a jihar Kaduna bayan da tawagar jami’an tsaro ta hadin gwiwa suka kai samame a maboyar ‘yan bindiga da ke karamar hukumar Igabi a ranar Juma’a.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Kaduna, Muhammed Jalige, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.
A cewarsa jami’an sun kashe wani dan bindiga, an kuma kama wasu mutane biyu da ake zargi, yayin da ‘yan fashin daji da dama suka tsere da raunukan harbin bindiga.
Ya bayyana cewa, tawagar jami’an tsaro sun kai farmaki dajin Sabon Birni a karamar hukumar Igabi a jihar da misalin karfe 2 na rana a ranar 31 ga watan Disamba 2021 bara.
Hakan ya biyo bayan rahotannin sirri da ke nuna cewa wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu domin neman kudin fansa a dajin.
Takwas daga cikin wadanda aka ceto an sake haduwa da iyalansu yayin da dayan ke ci gaba da karbar magani.
Comments 1