Daga Sulaiman Musa
Jami’an tsaro a ranar Alhamis sun dakile yunkurin fursunoni na balle gidan yarin Kurmawa da ke daura da fadar sarkin Kano.
Kakakin hukumar gyara halinka (NCS) reshen jihar Kano, Musbahu Lawan, ya bayyana wa manema labaru cewa yunkurin balle gidan yarin ya biyo bayan sa’ayin da fursunonin da aka yanke wa hukunci suka kitsa ne.
Lawan ya kuma ce tashin hankalin ya fara ne a daidai lokacin da jami’an tsaron gidan yarin suka hana shiga da miyagun kwayoyi ciki har da wayoyi ga wadanda ake tsare da su a gidan yarin.
Ya nuna cewa hana shiga wa masu laifin da miyagun kwayoyin da suke so ne ya tunzura su yin bore da neman arcewa, sai dai hukumomin tsaro sun tabbatar da yin duk mai yiyuwa domin hana hakan faruwa.
Sai dai ya kartaya jita-jitan da ke cewa, fursunonin sun yi zanga-zanga ne sakamakon karancin abunci da suke samu, ya ce sam zancen ba haka yake ba.