By Abbas Yakubu Yaura
Aikin hadin gwiwa da jami’an tsaro suka yi da sanyin safiyar Lahadi a kananan hukumomin Jibia da Danmusa na jihar Katsina sun yi nasarar kwato dabbobin gida guda 102 daga hannun ‘yan bindiga bayan musayar wuta da suka yi.
Jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda, sojojin Najeriya da ‘yan banga sun kai farmaki kauyukan Kadoji da Megezoji dake karamar hukumar Jibia da Danmusa a safiyar ranar Lahadi inda suka tarwatsa ‘yan bindigar tare da kwato dabbobin da aka sace daga sansaninsu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Katsina, SP Gambo Isah ya tabbatar da faruwar lamarin a safiyar ranar Litinin.sannan ya yi bayanin cewa aikin ya samo asali ne daga sahihan bayanan sirri kan ayyukan ‘yan bindiga a sansanin su da ke cikin garuruwan biyu.
Isah ya kara da cewa bayan artabun harbe -harben bindiga, jami’an tsaro sun samu nasarar fatattakar ‘yan bindigan tare da kwato shanu 43,da Awaki 47 da raguna goma sha biyu.Sai dai kuma bai bayyana cewa ko an kama wani daga cikin ‘yan bindigar ba.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “A ranar Lahadi, 24/10/2021 tsakanin sa’o’i 1130 zuwa 1315, bisa la’akari da sahihan bayanan sirri,da rundunar hadin gwiwa ta ‘yan sandan Nijeriya, data Sojojin Najeriya da kungiyar ‘yan banga sun kai hare -hare a kauyen Kadoji, Jibia, sansanin wani sanannen ɗan fashi, Bala Wuta.
A sakamakon haka, bayan musayar wutar da aka yi tsakanin ‘yan bindigar, jami’an tsaro sun fatattaki maharan da tawagarsa.inda Tawagar ta yi nasarar lalata sansaninsa tare da kwato shanu goma sha biyar (15), awaki ashirin da takwas (28) da raguna goma sha biyu (12) wadanda ake zargin sun sato sune.
Hakazalika, Kwamandan Yankin, Dutsinma, ya jagoranci tawagar yan sanda zuwa sansanin yan bindigan Megezoji dake dajin Yantumaki, inda suka tarwatsa yan bindigan, suka lalata sansaninsu tare da kwato shanu ashirin da takwas (28) da awaki goma sha tara (19), wadanda ake zargin suma na sata ne”.
Wadanda ake zargin sun hada da wani matashi dan shekara goma sha hudu da ake zargin barayin shanu ne da wani mutum mai shekaru 25 da ake zargi ya kitsa sace mahaifinsa akan kudin fansa naira miliyan 2.