Jami’an tsaro a ranar Alhamis din nan sun rufe shedikwatar jam’iyyar NNPP da ke Maiduguri a jihar Borno.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Lamarin wanda ofishin yada labarai na dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Rabiu Kwankwaso ya tabbatar, ya kuma ga jami’an tsaro na fatattakar wasu ma’aikatan jam’iyyar.
“Da safiyar yau ne tawagar jami’an tsaro karkashin MOPOLS na ‘yan sandan Najeriya suka rufe shedikwatar mu ta karfi da yaji, sun lalata kayayyakin aiki, da duka, da raunatawa, tare da fatattakar gungun ma’aikata, ‘yan jam’iyya, da magoya bayansu,” in ji ofishin yada labarai na Kwankwaso. sanarwar da Muyiwa Fatosa ya fitar, kamar yadda gidan talabijin na channels ya rawaito.
Karanta kuma: Kwankwaso ya isa gidan Shekarau domin tattaunawar ƙarshe kan koma wa NNPP
“Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban jam’iyyar NNPP na kasa da kuma dan takarar shugaban kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, Ph.D FNSE ya kai ziyara jihar Borno domin kaddamar da ofishin a cikin kwanaki biyu, daga Asabar 27 ga Agusta 2022.”
Ofishin yada labaran, wanda ya bayyana lamarin a matsayin “abin da ba za a amince da shi ba kwata-kwata”, ya yi kira ga gwamnati da ta shiga cikin lamarin.
“Wannan matakin ba shi da karbuwa kwata-kwata kuma muna Allah wadai da shi gaba daya. Sanarwar ta kara da cewa a fili tana aikawa yin abun daidai ba yayin da muka shiga wani mawuyacin hali na lokacin zaben.
“Saboda haka, muna kira ga gwamnatin jihar Borno da ta bada umarnin a dawo mana ofishinmu, sannan ta umurci jami’an tsaro da ke can su fice daga harabar mu. ‘Yan sanda da jami’an tsaro dole ne su bijirewa duk wani yunƙuri na yin amfani da su a matsayin makami daga wasu ‘yan siyasa.”
Don haka, ta yi kira ga magoya bayan jam’iyyar da su kwantar da hankulan su, tare da tabbatar da cewa hakan ba zai sa ‘yan jam’iyyar NNPP da kuma Sanata Kwankwaso su karaya ba.
“Muna kira ga dukkan magoya bayanmu da su kwantar da hankalinsu, masu bin doka da oda, su ci gaba da harkokinsu daban-daban, musamman jam’iyyarmu da magoya bayanmu a jihar Borno da su ci gaba da shirye-shiryen karbar dan takararmu na Shugaban kasa nan da kwanaki biyu, a Asabar 27 ga watan Agusta, 2022. ” ya kara da cewa.
A wani labarin kuma: Zaben 2023: Ba Mu Rena Karsashin PDP, Da APC Ba, Amma Jam’iyar NNPP Zata Bada Mamaki—–Kwankwaso
Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP karkashin jagorancin Rabi’u Kwankwaso, ta ce ba ta manta da karfin jam’iyyar PDP da APC ba, sai dai tana shirye shiryen ganin ta bada mamaki. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito
Shugaban jam’iyyar na kasa Farfesa Rufa’i Alkali ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a ranar Laraba a Legas.