Wata gamayyar Jami’an sun hallaka wasu ƴaƴan Ƙungiyar Inyamurai ta IPOB a daren jiya Alhamis yayin da suka kitsa kai wani mummunan farmaki a ofishin yan sanda na Orlu Division dake Jihar Imo.
Kazalika Jam’ian Tsaron sun yi nasarar karɓe motoci bakwai da yan ta’addan IPOB din suka yi amfani da su don kai harin.
Wannan farmaki na zuwa ne kwana guda bayan da sabon Kwamishinan Yan Sanda na Jihar Abutu Yaro ya karbi ragamar aiki.
Gabannin Hallaka mutanen sai da aka shafe sa’o’i ana musayar wuta tsakanin yan IPOB din da Jami’an tsaro, lamarin da ya kai ga sai da aka sake aike da jami’an soji daga runduna ta 34 dake Obinze na birnin Owerri fadar gwamnatin jihar.
Wani mazaunin yankin da ya so a sakaye sunan shi, ya ce al’ummar yankin sun kwana cikin fargaba sakamakon ɓarin wuta da suka ji ana ta yi.
Har kawo lokacin da muke baku wannan labarin, ba a samu ji daga bakin Kakakin Rundunar Yan Sandar Jihar ba, to amma wata majiya daga jami’an yan sandsr ta tabbatar da aukuwar wannan lamari.
Idan ba a mance ba a watan Afirelu ne dai wasu yan ta’adda da ake zargin yan kungiyar Inyamurai ta IPOB ne suka kutsa gidan yarin jihar ta Imo inda suka saki dubban fursunoni.