Jami’an tsaro a ranar Laraba sun hana Maxwell Opara, ɗaya daga cikin Lauyoyin dake kare tsararren Shugaban Ƙungiyar Ƴan Aware ta Inyamurai — IPOB Nnamdi Kanu, daga shiga Babbar Kotun Tarayya dake Abuja.
Haka zalika, waɗanda aka hana shiga Kotun akwai ƴan jarida, da Shuwagabannin Inyamurai, da masu sanya ido gami da masu kare haƙƙin bil’adama.

KARANTA WANNAN LABARIN: Muna Bukatar Aure, Inji Jaruma Rashida Adamu Abdullahi
Amma sauran Lauyoyin Kanu da suka haɗa da; Ifeanyi Ejiofor, da Aloy Ejimakor an barsu sun shiga a cikin Kotun.
Idan dai ba’a manta ba, Mai Shari’a Binta Nyako ta ɗage shari’ar Kanu zuwa ranar Yau.
Kanu dai na fuskantar ƙararraki, kuma tuni ake tsare dashi a kurkukun Hukumar Jami’an tsaron Ƴan sandan Farin Kaya, tun lokacin da aka sake kama shi a ƙasar waje a watan yunin shekarar 2023.
Ya kuma bayyana cewa bai aikata laifuka guda 7 da ake zargin shi da aikatawa a zuwan shi Kotu na watan Oktoba na shekarar 2021.