Jami’an tsaron Rundunar kankace Kwabo na Sojin Sama dake da Sansanin a Gusau, a ranar Talata, sun kama kimanin Lita 1,000 na Man Gas din Mota, zuwa wani wurin da ake zargin sansanin ‘yan bindiga ne.
Mai ba Gwamnan Jihar Zamfara shawara na musamman kan harkokin tsaro, Abubakar Dauran ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
Ya bayyana cewa an kama direban motar, Mai suna Garba Noma da wasu mutane guda Biyu da suka hadar da Abubakar Mohammed da Haruna Idris da ganguna hudu cike da Man Gas a cikin motar.
Mista Dauran ya ce, an mika wadanda ake zargin ga jami’an da ke sa ido domin gudanar da bincike, tare da daukar matakin da ya dace.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jirgin Ruwa Dauke da Bakin Haure 27 ya Nitse a Tekun Turkiyya
Kwamandan Bataliyan na 207 Captain Daniel Komo ya jaddada aniyar rundunar sojojin saman Najeriya na hada kai da sauran jami’an tsaro, domin kawar da ‘yan bindiga baki daya a jihar.
A baya dai gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da daukar matakan tsaro da za su taimaka wajen rage aiyukan ‘yan bindiga a jihar, da suka hada da hana siyar da man fetur a Jarka, gwangwani, da dai sauran su.