Rundunar Sojin Najeriya da sauran Hukumomin tsaro sun Kama Godwin Nnamdi, Shugaban Ƙungiyar Ƴan Aware na IPOB dake kula da jami’an tsaron su.
Nnamdi, da aka bayyana a matsayin “ƙasurgumin mai laifi” an kama shi ne a Ƙaramar Hukumar Nkanu ta Gabas.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Rundunar Soji Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu ya fitar, yace dakarun soji dake aiki a tawaga ta 82 suka jagoranci kai samamen.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wata Sabuwa: Matsafi ya mutu a hannun Ƴan Sanda a Ondo
An kama Nnamdi a lokacin wani samame a sansanin IPOB/ESN dake a dajin Akpowfu na Ƙaramar Hukumar Nkanu ta Gabas.
Jami’an tsaron sunyi musayar wuta, inda suka kashe shugaban ƙungiyar nasu, bayan yaran shi sun tsere cikin daji.
Bindiga ɗaya, da kwafsar harsashi mai gudana 21 da waya guda ɗaya an same su a tattare dashi.
Babban Hafsan Sojin Ƙasa Laftanar-Janar Faruƙ Yahaya ya yabawa jami’an da irin wannan gagarumar nasara.