Ma’aikatar harkokin cikin gida ta Kenya ta ce, an samu nasarar kwato bindigogi akalla 200 da kuma daruruwan harsasai a lardin Marsabit da ke arewacin kasar, a ci gaba da aikin samar da zaman lafiya a yankin.
Fiye da bindigogi 5,000 ne aka kwace, da ake zargin an Mallaka ta haramtacciyar hanya a cikin al’umma, in ji sakataren harkokin cikin gida na kasar, Fred Matiang’i.
Tawagar jami’an tsaro ta hadin gwiwa na gudanar da samame na kwace makamai daga hannun jama’a.
Jami’ai sun ce an mika musu wasu bindigogin da aka kwato.
Gwamnati ta kuma tsawaita dokar hana fita daga yamma zuwa wayewar gari na tsawon kwanaki 30. Tuni dai karamar hukumar ta kasance karkashin dokar ta-baci tsawon watanni biyu da suka gabata.
A halin da ake ciki kuma, rikicin kabilanci a yankin arewacin kasar ya riga ya yi sanadin asarar rayuka da dama, kuma rikicin baya-bayan nan da ya barke ana alakanta shi da tada zaune tsaye a siyasance, yayin da ake cigaba da yakin Neman zabe, da za’a gudanar a watan Agusta mai zuwa.
Haka kuma yankin yana fama da matsanancin karancin abinci a ‘yan watannin nan.
Duk da haka, karancin abincin ya haifar da matsala ga albarkatun da aka raba kamar ruwa da kiwo tare da jefa iyalai cikin hadarin yunwa.