Rundunar soji ta Operation Safe Haven ta kama ‘yan bindiga takwas da ake zargi da kashe-kashe a ƙauyukan dake Kudancin Kaduna.
An kuma harbe ɗaya daga cikin ‘yan bindigar a ƙoƙarin kama su.
Kwamandan Rukunin Soji ta biyu, da ke kula da Kudancin Kaduna, Kanar David Nwakonobi, a lokacin gabatar da ‘yan bindigar a Kafanchan ya danganta nasarar kamo su da bayanin sirri na ƙwarai da aka ba su.
“Ranar 5 ga watan Agusta sojojinmu suka yi amfani da bayanan sirri na kwarai suka kamo wadanda ake zargin ‘yan bindiga ne mutum shida a Karamar Hukumar Lere ta Jihar Kaduna.
https://dimokuradiyya.com.ng/yan-bindiga-sun-hallaka-mutum-33-a-zangon-katat-na-jihar-kaduna/
“Sojojin da taimakon ‘yan banga sun kuma kamo wasu mutum biyu da ake zargin ‘yan bindiga ne a ƙauyen Chawai da ke tsakanin ƙananan hukumomin Kauru da Zangon Kataf”, inji kwamandan
Nwakonobi ya ce sun kama su da bindigogi ƙirar gida guda biyu samfarin (Pump Action Guns) da ƙananan bindigar bindigar biyu, su ma kirar gida da harsashi da adduna da sauran makamai.
Kwamandan ya ce za a miƙa su hannun ‘yan sanda domin ci gaba da bincike.
Nwakonobi ya kuma ƙara bayar da tabbacin za su ci gaba da aiki tare da mutanen garuruwan domin kawo ƙarshen kashe-kashen da ake gama da su a yankin.