Jami’an tsaro da suka haɗar da Ƴan sanda, da jami’an SSS da kuma na Hukumar yaki da cin hanci da aikatawa rashawa EFCC sun yiwa gidan Mary Odili ƙawanya a ranar juma’a, domin gudanar da bincike a gidan.
Mary Odili dai ta kasance Alkaliya a kotun daukaka kara dake birnin tarayya Abuja, kuma mata ga tsohon gwamnan jihar Rivers, Sanata Peter Odili, wanda kuma mijin nata yana daga cikin wadanda hukumar EFCC ta sanya a komar ta.
Wata majiya ta tabbatar da cewa jami’an tsaron wadanda cikin su har dana soji, sun bayyana cewa su mambobi ne ja hadakar jami’an tsaron kar ta kwana, kuma sun je gidan ne bayan da suka samu rahoton aikata abubuwan da basu kamata ba a cikinsa.
Mary Odili dai ana hasashen zata kasance daga cikin Alkalai 7 da za a nada domin yanke hukunci kan harajin kayayyaki na (VAT) Wanda ake cigaba da samun takaddama tsakanin gwamnatin Tarayya da ta jihohi dangane da batun mallakarsa.