Wani abu mai kama da Wasan kwaikwayo ya faru a majalisar dokokin Filato, inda Zanga zangar da wasu matasa suka yi, ya dauki wani yanayi mai ban tsoro a yau.
Sakamakon yanayin kasancewar da rikicin yayi tsakanin masu Zanga zangar ya sanya jami’an tsaro suka yi awon gaba da tsigaggen kakakin majalisar Abok Ayuba da wasu ‘yan majalisa 10 da ke masa biyayya.
Da misalin karfe 3:15 na rana, kwamishinan ‘yan sandan jihar Filato, Edward Ebuka, ya jagoranci ‘yan wasu mutane 11 zuwa motocin Hilux guda hudu tare da jira a gefe tukunna, kafin daga bisani jami’an tsaron su tafi da su.
Memba mai wakiltar Langtang ta Kudu, Honarabul Zingtin Sohchang ya ce: “Yanzu jami’an tsaro sun hada mu a cikin motocin Hilux hudu har yanzu ba mu san inda zasu kaimu ba, idan bayan mintuna 20 kuka kira mu ba amsa ba, to ku sani cewa an kai mu wurin wurin da ba a sani ba.”
Abok, da manema labarai suka tambaye shi akai-akai ko an kama shi, ya amsa: “Ba zan iya cewa Komai ba kan halin da nake ciki yanzu ba.”
Jami’an tsaro karkashin jagorancin kwamishinan ‘yan sandan ne suka yi awon gaba da shi da wasu ‘yan majalisar su 10 daga harabar majalisar.
Comments 1