Daga: Abbas Yakubu Yaura
An shiga cikin tashin hankali a wasu sassa na Abeokuta, babban birnin jihar Ogun a ranar Lahadin da ta gabata, biyo bayan kama wani da ake zargin shugaban kungiyar Boko Haram ne.
Wani gidan rediyo mai zaman kansa a Abeokuta ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi da yamma wanda ya haifar da firgici a tsakanin mazauna jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Babu Ja Da Baya Kan Yunkurin Tsige Buhari, Yanke Shawara Ce Ta Gamayya – Sanata Binos Yaroe
Rahotanni sun bayyana cewa jami’an hukumar tsaro ta DSS sun kama wanda ake zargin ne a daren ranar Asabar.
Wani sauti na labaran ya bazu a shafukan sada zumunta na jihar a ranar Lahadi.
Wannan ci gaban dai na da nasaba da shirin kai hare-hare a wasu jihohin Kudu maso Yamma da ake zargin ‘yan ta’adda ne.
Sai dai wata majiya mai tushe ta shaida wa wakilinmu cewa an kama wanda ake zargin shugaban kungiyar Boko Haram ne kwanaki a unguwar Ijaye da ke Abeokuta.
Majiyar ta ce tun da farko wanda ake zargin ya yi turjiya kafin ya mika wuya ga karfin jami’an DSS.
A cewar mai binciken, an gudanar da aikin ne a daren ranar Asabar.
A rahoton da gidan rediyon ya bayar, an ce dan ta’addan da ake zargin ya isa Abeokuta ne daga jihar Katsina, inda ya yi aikin tsaro a Ijaye, inda ya ke tattara bayanan sirri kan hare-haren ta’addanci.
Majiyar tsaron ta ce, “Shi (wanda ake zargin) ya koma Abeokuta ne domin ya kafa kungiyar ‘yan ta’adda domin yin garkuwa da mutane da kuma kai hare-haren ta’addanci.
“Kuma bayan wani taron sirri da aka yi, jami’an tsaro dauke da bindigogi sun kai farmaki maboyarsa suka dauke shi.
“Ba abu ne mai sauƙi ba. A hankali da yardar Allah sun isa ga masu aikin.
“Har yanzu akwai da yawa daga cikinsu, amma muna kan gaba a wasanmu.”
Wakilinmu ya tattaro cewa wanda ake zargin yana hannun jami’an DSS har yanzu.
Da aka tuntubi Kakakin Hukumar DSS, Peter Afunanya, bai amsa sakon tes da aka aika a layin wayarsa ba.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya ce bai da masaniya kan kamun.