Jami’an tsaron sa kai a shiyyar arewa maso yammacin Najeriya sun ce sunyi nasarar halaka yan fashin daji fiye 200 a garin Malele na karamar hukumar Borgu a jihar Niger.
Kwamandan Rundunar tsaron ta sa kai mai lura da arewacin kasar nan Arama Ya’u Agawada shine ya sanar da hakan yayin da yake yiwa wakilin Jaridar Dimokuradiyya Ibrahim Hausawa, Wanda hakan wani bangare ne na irin nasarorin da jami’ansu suka samu a Jihar Neja.
Yace maharan da jami’an nasu suka kashe, na cikin wadanda suka addabi yankunan Onashi a jihar Kebbi da wasu yankuna na jihar Niger.
Kazalika bayan mika godiyarsa ga Allah da ya basu wannan nasara, ya kuma nemi hadin kan al’ummar kasar nan, don su ci gaba da yi musu addu’o’i don ci gaba da samun nasarar cimma abunda suka sanya gaba na murkushe aiyukan ‘yan ta’adda a sassan kasar nan daban-daban.
Comments 1