Kimanin matasa 1,056 da aka dauka aiki a matsayin Constabulary a cikin rundunar ‘yan sandan Najeriya domin baiwa ‘yan sanda damar tabbatar da tsaro a jihar Kwara sun gudanar da zanga-zanga a Ilorin.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Zanga zangar ta biyo bayan rashin biyansu albashin watanni 16 da gwamnatin jihar tayi.
‘Yan sandan sun gudanar da zanga-zangar ne a wurare masu muhimmanci na babban birnin jihar da suka hada da ofishin gidan waya da kuma hanyar Ahmadu Bello ta zuwa gidan gwamnatin jihar inda suka ce “gwamnatin jihar Kwara, ki biya mu albashin mu na tsawon watanni 16.
2023: Wasu Magoya Bayan Ka Makiya Ne, Obasanjo Ya Gargadi Tinubu
Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun hau babura dauke da mutane uku kowannen su, yayin da wasu da ke sanye da bakaken kaya na ‘yan sanda kuma suka rufe jikinsu da ganye yayin da suke tafiya kan tituna.
‘Yan sandan sun koka da cewa gwamnatin jihar ba ta biya su albashi ba tun bayan kammala horas da su a watan Afrilun 2021.
Sai dai rundunar ‘yan sandan jihar ta mayar da martani da cewa, rundunar ‘yan sandan jihar ko gwamnati ba su yi alkawarin biyan ma’aikatan albashi na wata-wata ba, kamar na ‘yan sanda na yau da kullum kafin lokacin horo da kuma bayan horar da su.
Sai dai kwamishinan yada labarai na jihar Mista Olabode Towoju ya ce kananan hukumomin jihar ne za su kula da ‘yan sandan.