Yan sanda a jihar Ogun sun bayyana cewa, sun cafke wani tsohon mai laifi, Mai suna Segun Ogundeji, wanda ya yi shigar burtu a matsayin soja Kuma ya shiga hedikwatar yan sanda na garin Sango-Ota da ke jihar Ogun.
Kakakin rundunar yan sanda a Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a garin Ota.
Oyeyemi ya bayyana cewa, an cafke Ogundeji lokacin da ya je Hedikwatar Runduna ta Sango-Ota, sanye da kakin soji, don neman a saki wani mutum da ake zargi.
KARANTA WANNAN LABARIN: An banka wa yan fashin POS wuta a Jihar Imo
Sanarwar ta ce, “Lokacin da ya isa tashar, Ogundeji ya hadu da wani Sojan Sama, Mai suna John Temitope, wanda ya zarge shi da gaza ba shi girma a hukumance, wanda a sakamakon haka rikici ya shiga tsakaninsu.”
“Rigimar ce ta sa jami’in‘ yan sanda na yankin wato DPO Sango-Ota, CSP Godwin Idehai, ya yi masu tambayoyi. A yayin da ake gudanar da bincike ne ‘yan sanda suka gano cewa, Ogundeji ba soja ba ne.
“An kuma gano cewa, wata kotu ta taba hukunta Ogundeji da laifin yin magudi, ” in ji shi.
A karshe Kwamishinan yan sandan jihar CP Edward Ajogun, ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike kan ayyukan Ogundeji.