Rundunar ‘yan sandan jihar Edo, a yau ranar Litinin, ta ce ta kashe wasu mutane biyar da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, tare da kwato makamai da kuma kubutar da mutum daya da aka aje shi a daji Ughoshi-Afe, Ibillo, a karamar hukumar Akoko-Edo ta jihar.
A wata sanarwa da mataimakiyar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, ASP Jennifer Iwegbu, ta fitar, ta ce an kashe wadanda ake zargin ne a wani artabu da bangarorin biyu suka yi.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Rundunar ‘yan sandan jihar Edo, a kokarinta na kawar da munanan laifuka musamman garkuwa da mutane a ranar Lahadin, ta ceto wani da aka yi garkuwa da shi, tare da kashe masu garkuwa da mutane biyar da kuma kwato makamai da alburusai.
“An samu wannan nasarar ne biyo bayan sahihin bayanan da aka baiwa rundunar cewa ‘yan bindigar da ake zargin masu garkuwa da mutane ne na gudanar da ayyukansu a dajin Ughoshi-Afe na garin Ibillo, a karamar hukumar Akoko-Edo, na jihar Edo.
Da Yuwuwar Diago Dalot Ya Koma Barcelona Yayin Da Aubameyang Zai Tafi United
“Bayan samun bayanin sirri, nan take rundunar ta tattara tawagarta daga Ibillo da kuma ‘yan banga da mafarauta zuwa wurin.
“Masu garkuwa da mutanen da suka ga jami’an ne suka bude musu wuta, lamarin da ya kai ga yin artabu da bindiga wanda ya yi sanadin raunata biyar daga cikin masu garkuwar kuma daga baya aka tabbatar da mutuwarsu. Wani da aka yi garkuwa da shi, Mista Innocent Achebe (mai shekaru 38), an kubutar da shi ba tare da jin rauni ba, kuma tuni ya koma gida domin sake saduwa da iyalansa.
Sanarwar ta kara da cewa “Abubuwan da aka gano a wurin sun hada da bindigogi biyu na gida, laya da kuma harsashi,” in ji sanarwar.