By Ishaq Dabai
An kama ‘yan sanda hudu a jihar Kogi da laifin karban Naira 25,000 daga hannun matafiyi yayin da suka ci zarafin wani a cikin wani faifan bidiyo da aka wallafa.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kogi, Idrisu Dauda Dabban ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin rundunar ‘yan sandan, William Aya, a ranar Lahadi.Mista Dabban yace, rundunar ta kuma fara gudanar da bincike kan bidiyon da ake zargin ‘yan sandan dake aiki a sashen rundunar ta Adogo.
A cewar sanarwar, ana zargin sun karbe Naira 25,000 daga wurin matafiyi sannan suka ci zarafin wani yayin da suke aikin sintiri a kan hanyar Adogo-Okene.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Kwamishinan, wanda ya yi Allah wadai da lamarin, yace an gano jami’an ‘yan sandan kuma an tsare su a sashen binciken manyan laifuka na jihar.
A cewarsa, jami’an sun hadar da Isah Barnabas, Ifediegwu Godwin, Emmanuel Ochima da Umameh Mathias.sannan yace an yiwa Mista Barnabas tambayoyi a hukumance yayin da kananan jami’ai uku ke fuskantar shari’ar (matakin horo na cikin gida na ‘yan sanda).
Kazalika kwamishinan ‘yan sandan ya lura cewa rundunar na yin iya bakin kokarinta don kulla hulda da wadanda abin ya shafa sannan ya umarce su dasu tuntubi rundunar ta lamba kamar haka 08107899269.
Mista Dabban ya ba da tabbacin cewa duk wani jami’in da aka samu yana da hannu a binciken za a yi maganinsa daidai gwargwado.