Rundunar ‘yan sanda a jihar Jigawa ta ce ta cafke mutane 14 da ake zargi da laifi a kananan hukumomin Gumel da Kazaure na jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Lawan Shiisu ne ya tabbatar da kamun ga Kamfanin Dillancin Labarai na Nigeria NAN, a Dutse Babban Birnin jihar, a yau Asabar.
Shiisu ya ce, an kai samamen ne a wasu maboyar masu laifin, inda aka kama wadanda ake zargi.
“An kai samamen ne a maboyar masu aikata miyagun laifukan, wanda ya kai ga cafke mutane 14 da ake tuhuma, Wanda Kuma aka baje kolin su a kananan hukumomin Gumel da Kazaure.” Inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jami’an Kwastam sun sake Harbe wani a katsina
“An kama wasu gayyayyaki da ake Zargin Wi-wi ne, da, babura biyu, da ba a yi wa rajista ba, da sauran su,” a cewar shi.
Mai magana da yawun rundunar ya ce, kwamishinan ‘yan sandan jihar,, Aliyu Sale, ya shawarci masu aikata laifuka a jihar da su gyara laifukan su, in ba haka ba za su fuskanci hukuncin, saboda babu wurin buya gare su.
Kazalika Kwamishinan, ya yi alkawalin kai samame ba kaukautawa ga maboyar masu aikata manyan laifuka a dukkannin faɗin jihar, don fatattakar masu aikata miyagun laifuka a jihar.