By Abbas Yakubu Yaura
Jami’ar jihar Abia, Uturu, ta kori wani babban malami, Michael Ukaegbu, bisa badakalar yin lalata da daliba wajen bata maki.
A cikin sanarwar bayan taro karo na 148 na yau da kullum da majalisar gudanarwar jami’ar ta gudanar a ranakun Alhamis 16 da 20 ga watan Disamba 2021, karkashin jagorancin shugaban jami’ar Adolphus Wabara, majalisar ta ABSU ta amince da korar Ukaegbu, tsohon shugaban riko na Sashen Sadarwar jami’ar
Sanarwar mai dauke da sa hannun magatakardar jami’ar, Acho Elendu ta kuma bayyana cewa majalisar ta kuma amince da korar wani, Mista Leonard Chukwuma bisa laifin badakalar bada izinin daukar dalibai da kuma zamba.
Wani babban jami’in gudanarwa na jami’ar ya shaidawa manema labarai cewa jami’an ABSU da jami’an tsaro sun yi ta bin diddigin malamin.
Majiyar tace daga baya, an kafa kwamitin ladabtarwa, wanda ya aike da rahoton nasu ga majalisar tare da jin dadin shawarwarin, wanda majalisar ta amince da shi.
Comments 1