Majalisar Dattijan tarayya ta sanya hannu kan takardar koran wasu daliban jami’ar Abuja kimanin 46 bisa samun su da laifuffuka da suka saɓa wa dokar makarantar.
Kazalika Jami’ar ta dakatar da karin wasu biyar na tsawon zangon karatu guda, yayin da Shari’ar wasu uku kuma aka sanarda cewa za a sake nazartar ta, da kuma bakwai da aka kori kararsu bayan da aka wanke su.
Wata Sanarwa daga Shugaban Sashen yada labarai da hulda da jama’a na Majalisar Dakta Habib Yakoob ta ce majalisar ta yanke wannan hukunci ne a wata zama da ta saba yi wacce ta gudana a ranar 27 ga watan Mayun wannan, inda ta nazarci korafe-korafe da kwamitin ladabtarwar jami’ar ya gabatar mata.
Daliban dai sun fito ne a tsangayoyi mabanbanta, yayin sanarwa ta ce 15 daga daliban suna zangon karshe, 20 zangon kusa da karshe, yayin da 8 daga cikin su ke aji na biyu a jami’ar sai kuma 100 dake aji na farko.
Kuma tuni Jami’ar ta umarci daliban da su gaggauta mika duka wani abin da ya shafi makarantar wanda ke wurin su kafin nan wuri ya kure musu.
Kazalika an umarce su da su gaggauta tattara nasu-ya-nasu su yi tafiyar toka daga kewayen jami’ar don gudun abinda zai kai ya komo.
Daga bisani jami’ar ta ce za ta hukunta duk wani wanda ta kama da aikata mummunar laifi, domin ba za ta bari a shafa mata kashin kaji ba.