Farfesa Solomon Adebola, a ranar Asabar an kaddamar da shi a matsayin shugaban Jami’ar Adeleke dake garin Ede a jihar Osun.
Da yake jawabi a wurin kaddamarwar a harabar Jami’ar, Adebola ya tabbatar da cewa zai tabbata da Jami’ar ta bayar da nagartaccen ilimi ga al’umma.
Farfesa Adebola, wanda shi ne tsohon mataimakin shugaban Jami’ar, ya kara da cewa zai tabbata da a karkashin kulawarsa an gudanar da jami’ar ba tare da wata tangarda ba.
Adebola ya ce zai gudanar da aikinsa cikin gaskiya da rikon amana, kuma zai tabbata da ganin Jami’ar ta cimma nasarar manufofin kafa ta.
A karshe ya jinjinawa hukumar Jami’ar bisa wannan dama da ta ba shi.