Jami’ar Al Qalam dake jihar Katsina ta yi fatali da jita-jitar harin bam da ake yadawa a shafukan sada zumunta, inda ta bayyana shi a matsayin “abin takaici ne, mara tushe, karya da kuma yaudara.”
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban sashen hulda da jama’a na cjami’ar, Akilu A. Atiku ya sanyawa hannu kuma ya fitar.
Sanarwar ta kara da cewa, “Abin da ya faru shi ne, tayar motar ce ta fashe a kan Titin Dutsamma da misalin karfe 8:30 na dare amma ‘yan masu yada jita-jita, sun yi amfani da lamarin wajen yada jita-jitar fashewar bam a cikin Jami’ar.
Jami’ar ta yi kira ga jama’a da su yi watsi da bayanan karya wadanda Basu da tushe balantana makama.