Jami’ar Obafemi Awolowo dake Ile-Ife ta sake dakatar da wani malami mai suna, Monday Omo-Etan, kan zargin laifin cin zarafin wata daliba mai shekara 19, wacce take karatu a sashen karatun gata.
Sanarwar dakatar da malamin ta fito ne daga hannun jami’in hulda da jama’a na jami’ar, Abiodun Olarewaju, wanda ya fitar a daren Laraba a garin Ile-Ife.
Abiodun Olarewaju ya ce, jami’ar ta gano hakan ne kasa da makonni uku da korar Olabisi Olaleye, malami a sashen huldar kasashe na jami’ar.
A cewarshi, Jami’ar Obafemi Awolowo ba za ta taba saurara wa masu cin zarafin dalibai ba.