Jami’ar Ekiti ta cire kan ta daga yajin aikin ASUU, ta sanar da ranar cigaba da Karatu
Jami’ar Jahar Ekiti dake Ado-Ekiti (EKSU) ya sanar da cewa harkokin Karatu zai cigaba a ranar Talata 24 ga watan Mayu.
Bode Olofinmuagun Daraktan kula da Harkokin Al’umma ya sanar da hakan a ranar Litinin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Boko Haram ta kashe Mayaƙan ISWAP 6, a wani rikici daya ɓarke tsakanin su
Yanke hukuncin ya biyo bayan wani taro da aka gudanar a ranar Litinin.
Olofinmuagun yace tattauna matsalolin da yajin aikin ASUU ya haifar ga dukkanin Ƙungiyoyin guda huɗu.
Ƙungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU ta fara yajin aiki a ranar Fabrairu na Shekarar 2022.
Mai Magana da Yawun Jami’ar yace Shuwagabancin Makarantar yana sane da irin baƙin ciki da Ɗalibai da Iyaye ke fuskanta.
Ya bayyana cewa har yanzu zangon Karatu na (2021/2022) ba a kaiga fara shi ba, a yayinda har yanzu Samista ta biyu a zangon Karatu na 2020/2021 ba’a kammala shi ba.
Haka zalika nan da wani lokaci za’a fara ɗibar Ɗalibai zuwa ga Zangon Karatu na Shekarar 2022/2023.
Yace Makarantar ta bude Makarantar ne domin Ɗalibai, Iyaye, Al’umma da kuma ɗorewar Cigaban ta.