Jami’ar Fasaha ta Gwamnatin Tarayya dake Owerri, Jahar Imo da gidauniyar Victoria-Nwaeke Research Foundation zasu cigaba da wayar wa Al’umma kai akan cutar Cancer wanda akafi sani da ciwon Daji, domin magance ta a Nahiyar Afirka.
Dayake jawabi a ranar Juma’a a lokacin bikin bayar da lambar yabo ga wasu ɗalibai da sukayi zarra wajen rubutun su na bincike na Kammala karatu a sashen Nazarin kayayyakin gwajin lafiya na shekarar 2019 zuwa 2020, Jami’in gidauniyar Abdulhakeem Abioye yace da ingantattun kayayyaki, nahiyar Afirka zata iya magance cutar Cancer.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu Ta Tasa Keyar Wani Mutum Mai Shekara 40 Gidan Kaso Bisa Laifin Yiwa ‘Yarsa Mai Shekara 5 Fyade A Jihar Ribas
Yace gidauniyar su ta TVN a shirye take wajen kawo ƙarshen cutar a Afirka da sauran cututtuka dake damun nahiyar, ta hanyar bincike da bada gudunmawa ta ilmi dake da manufar samar da hanyar kawar da cutar.
Yace wannan taron karrama wa da ake tunani zai zama na farko na shekara, hakan zai samar da kayayyakin fasahohi da zai kawo ƙarshen cutar a ƙasar da nahiyar baki ɗaya.
Yace injin “Thermal ablation shine Wanda aka tabbatar yana da ƙarfin magance cutar cancer.
Yace gidauniyar na fatan ta cimma nasara ta ɓangaren bincike da suke da sauƙi wajen magance matsalolin dake fuskantar Nahiyar Afirka.
A jawabinshi, Shugaban sashen Nazarin Kimiyyar kayayyakin lafiya na Jami’ar T. O Azeez yace ɗaluban da suka yi zarra kuma aka zaɓe su, anyi hakan ne bayan bincike mai zurfi akan al’amuran da suka shafi Nahiyar Afirka.
Yace jami’ar a shirye take wajen haɗa hannu da gidauniyar domin magance ciwon daji-Cancer a nahiyar Afirka.