Jami’ar gwamnatin tarayya dake Dutse, ta ayyana ranar 1 ga watan Fabarairun 2021 a matsayin ranar homawa makaranta.
Kakakin jami’ar, Abdullahi Yahya Bello ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce hukumar Jami’ar ta amince da a dawo makaranta a wannan rana.
Ya kara da cewa ba da jimawa ba za a fitar da tsarin yadda karatu zai ci gaba.