Hukumar gudanarwar jami’ar Ambrose Alli da ke Ekpoma a jihar Edo ta kori wasu malamanta hudu bisa zarginsu da aikata mugun aiki.
Kwamitin Sulhu na Jami’ar wato SIT ce ta korar malaman, bayan da ta yi la’akari da rahoton kwamitin ladabtarwa na manyan ma’aikatan jami’ar (SSDC) a yayin taronta na gaggawa.
Malaman da aka kora sune Engr. Lawrence Imaekhai; Engr. Dr Sumaila O. Jimoh; Engr. Haruna Andrew Idoko, dukkansu daga Sashin Injiniya da Fasaha da Barr. Patrick Ikechuckwu Iweoha, daga sashin Shari’a.
Jami’in hulda da jama’a na jami’ar Edward Aihebva ne ya tabbatar da sallamar malaman.
Ya ce, “An kori Malamai hudu saboda rashin da’a. Kuma an tura Al’amarinsu ga babban kwamitin ladabtarwa na ma’aikatan jami’ar, wanda ya ba da shawarar ga Tawagar Sashi na Musamman, kuma SIP ta yi aiki da shi.”inji shi.