Jami’ar jihar Kaduna ta bada umurnin ma’aikatanta na wucin gadi su tafi hutun dole sakamakon cutar Korona ba tare da ta biya su ba.
Magatakardar Jami’ar, Samuel Manshop, shi ne ya tabbatar da hakan a wata takarda da ya sanyawa hannu a ranar Alhamis a Kaduna, inda ya ce wannan hutun dolen ga ma’aikatan dole ne ya fara aiki daga 1 ga watan Mayu.
Sai dai ya tabbatar musu da cewa albashinsu da aka rike na watannin Maris da kuma Afrilun 2020, za a biya su da zarar Jami’ar an ba ta kasonta.
Amma ya tabbatar musu da cewa za a sanar da su ranar da za su dawo daga wannan hutun na dole, inji Samuel Manshop.
Ya nemi da su mika dukkanin wani tarkacen jami’ar dake hannunsu ga Daraktan sashen lura da lafiya na Jami’ar.