A wani mataki na ganin an kare lafiya da rayukan dalibai, Jami’ar Jos ta bada umarnin rufe dakunan dalibai a Makarantar.
Cikin wani sanarwa a Facebook da aka wallafa ta shafin Mataimakin Magatakardan Jami’ar Abdullahi Abdullahi ya ta ce majalisar dokokin kasa ita ma ta amince da wannan mataki.
Sanarwar ta ce dukkanin dakunan Kwanan Dalibain za su ci gaba da zama a rufe har sai abinda Kwamishinan Yan Sandar Jihar ya ce.
Kazalika ta ce matakin rufe dakunan ba a yi shi gaba gadi ba face da sanin shugabannin dalibai da kuma Kwamishinan Yan Sandar.
Idan jama’a ba su manta ba dai a makon da ya gabata ne wasu yan bindiga suka yi garkuwa da wata malamar jami’ar da mai gidanta inda har kawo yanzu babu su babu labarin su.