Hukumar gudanar da Jami’ar Maryam Abacha dake Maradin Jamhuriyyar Nijer (MAAUN) ta jajantawa iyalan tsohon dan majalisar tarayya mai wakiltar Gwarzo/Kabo, Marigayi Hamza Zakari Gwarzo.
Marigayi Zakari Gwarzo ya rasu ne a garin Gwarzo a ranar Litinin din 14 ga watan Disambar 2020 yana da shekaru 70 a duniya bayan gajeruwar rashin lafiya.
Sakon ta’aziyyar na dauke ne a cikin wata takarda da shugaban Jami’ar MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya sanyawa hannu ya kuma rabawa manema labarai a ranar Alhamis a Kano.
Abubakar-Gwarzo, ya bayyana rasuwar tsohon dan majalisar a matsayin wani rashi babba da aka yi, wanda ya ce rashin ba kawai ga iyalan mamacin bane, ga daukacin al’ummar Gwarzo da Kabo da ma jihar Kano baki daya ne suka yi rashi.
“a yau mun rasa Dattijo kuma Uba, Alhaji Hamza Zakari Gwarzo, wanda ya kasance dan majalisar tarayya mai wakiltar Gwarzo/Kabo daga shekarar 1999 zuwa 2007”. Inji sanarwar.
Abubakar-Gwarzo, ya bayyana mamacin a matsayin Dattijon kwarai, ya kuma yi masa addu’ar Allah ya jikansa da Rahama, ya kuma Rahamshe shi, ya sanya shi a aljannah Firdaus tare da bai wa iyalai hakurin jure wannan rashin da aka yi.
Marigayin ya rasu ya bar mata biyu da kuma ‘ya’ya 22, kuma tuni aka bizne shi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a garin Gwarzo.