Hukumar gudanarwa ta Jami’ar Maryam Abacha American University dake Maradi a Jamhuriyyar Nijer (MAAUN) ta mika sakon jajenta ga gwamnatin Jamhuriyyar Nijer, iyalai da ‘yan’uwa da abokan arziki bisa rasuwar Mohamed Ben Omar, ministan kwadago na kasar wanda ya rasu a babban asibitin birnin kasar ta Niamey a ranar Lahadi.
Sakon ta’aziyyar na kunshe ne a cikin sanarwar da shugaban Jami’ar ta MAAUN din, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya sanyawa hannu ya kuma rabawa manema labarai a Kano a ranar Litinin.
Farfesa Abubakar-Gwarzo ya bayyana rasuwar Ben Umar a matsayin wani babban rashi ba kawai ga iyalansa ba, ga kowa da kowa dake Jamhuriyyar Nijer musamman duba da gudummawarsa wajen ci gaban ilimi a lokacin da yake ministan ilimi na kasar.
“Muna cikin bakin cikin samun labarin rasuwar Ben Omar Mohamed, wanda har zuwa rasuwarsa, ya rike mukamin ministan ilimin manyan makarantu sannan ya zama ministan kwadago na jamhuriyyar Nijer.” Inji Farfesa Abubakar-Gwarzo.
Ya bayyana rasuwar Mohamed a matsayin barin wani babban gibi ba kawai ga iyalinsa ba, ga ma kasar Jamhuriyyar Nijer baki daya.
“A madadin kwamitin amintattu da hukumar gudanarwa na Jami’ar Maryam Abacha dake Nijer, muna mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalai da kuma dukkanin al’ummar Nijer bisa rasuwar minista.”
Daga karshe Farfesa Abubakar-Gwarzo ya yi addu’ar Allah ya jikansa da Rahama ya kuma bai wa iyalinsa hakurin jure rashin da suka yi.