Jami’ar Maryam Abacha American University dake Maradi a jamhuriyyar Nijar, ta bai wa wata dalibar Jami’ar kyautar naira miliyan daya sakamakon kammala Jami’ar da kyakkyawan sakamakon mai daraja ta daya wato ‘First Class’ a tsangayar shari’a.
Maryam Abdullahi Danbam wacce take ‘yar asalin jihar Kano ce, ta samu wannan kyautar ne daga shugaban Jami’ar, Farfesa Adamu Abubakar-Gwarzo, wanda ya ayyana kyautar a yayin da yake mika mata takardar shaidar kammala jami’ar a lokacin taron da aka shiryawa daliban da suka karanci bangaren shari’ar a ranar Alhamis.
Farfesa Gwarzo ya kara da cewa hukumar gudanar da Jami’ar ta kuma bai wa dalibar damar zuwa ta yi karatun digirinta na biyu kyauta a Jami’ar. A cewarsa, Maryam Abdullahi Danbam ta nuna kwazo da bajinta, inda ta kasance dalibar da ta fi kowa hazaka cikin dalibai 35 da suka kammala a wannan Tsangaya na shari’a a shekarar 2020.
Farfesan ya kara da cewa sun yanke wannan hukuncin bai wa Maryam kyautar kudin ne da kuma ba ta damar karatun digiri na biyu kyauta sakamakon kwazon da ta nuna domin karfafa sauran dalibai akan su maida hankali sosai akan sha’anin iliminsu.
Har wala yau Farfesa Gwarzo ya yi kira ga dukkannin daliban da ke Jami’ar da sauran ma wadanda suke sauran kasashen duniya da su yi koyi da dabi’ar jajircewa da sadaukarwa domin ganin sun yi nasara a karatun da suka sanya a gaba.

“ina mai kira ga dukkanin dalibanmu da sauran dalibai da ke sauran kasashen duniya da su jajirce da kuma sadaukarwa akan karatunsu domin ganin sun samu nasara.” Inji shi.
Da yake jinjinawa Maryam bisa dabi’arta da wannan nasara da ta samu, Farfesa Gwarzo ya shawarci sauran dalibai da su dabi’antu da dabi’a mai kyau, kuma su zama kyawawan jakadu ga Jami’ar a duk inda suka shiga.
Da take maida jawabi a madadin daliban, Maryam Abdullahi Danbam ta bayyana jindadinta tare da mika godiyarta ga hukumomin Jami’ar bisa ba ta wannan kudi da ba ta damar karatun digiri na biyu.
“Wannan shi ne ranar farin cikina a duniya. Ina son mika godiyata ga hukumar wannan Jami’a da kuma shugaba kuma mamallakin Jami’ar MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar-Gwarzo bisa wannan karamci.” Inji ta.
A karshe ta yi kira ga dukkan wadanda suke son zuwa Jami’a da su zo Jami’ar MAAUN, domin a cewarta ita ce Jami’ar da ta fi kowanne ba kawai a Jamhuriyyar Nijer ba, harda ma nahiyar Afrika baki daya.