Shugaban jami’ar Yusuf Maitama Sule dake nan Kano Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa ya sanar da cewa nan da zuwa sabuwar shekarar ta 2022 jami’ar zata fara bude tsangayar koyar da aikin lafiya domin amfanar daliban jihar Kano da kuma al’umma baki daya.
Farfesa Atiku Kurawa ya bayyana hakan ne a yau yayin bikin kaddamar da sabbin daliban da jami’ar ta dauka a kakar karatu ta 2021/2022 wanda yawan su ya kai dubu 5 da 60.

Ya kara da cewa karkashin mulkinsa zai yi kokari wajen cigaba da samar da fannonin ilimi da zasu taimaki daliban jami’ar su samu ilimin day a dace dai dai da zamani, tare da bukatar daliban da aka dauka su zama jakadu na gari da kuma biyayya ga dokokin jami’ar.
DUBA WANNAN LABARIN: Yan Bindiga sun sace mataimakin shugaban wata Sikandire a Abuja
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Yanzu dai jami’ar ta Yusuf maitama sule tana da tsagayoyi guda 6 da dalibai daban ke karatu karkashin su, tun bayan da aka samar da jami’ar a shekarar 2012.