Ɗan wasan gaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Leicester City kuma ɗan asalin ƙasar Ingila wato Jamie Vardy ya taras da tarihin da tsohon ɗan wasan ƙungiyar ƙaallon ƙafa ta Chelsea ya kafa wato Didier Drogba.
Ya taras da tarihinne a jiya bayan Lieceter City ta sami nasara awasanta na farko na gasar ajin Firimiya ta ƙasar Ingila da aka fara daci 3 da nema inda daga cikin ƙwallayen guda uku Vardy ne ya jefa guda 2.
Drogba bai ya buga wasanni 254 a gasar ta ajin Firimiya inda ya jefa ƙwallaye guda 104 kafin ya bar gasar ta Firimiya inda duka ya jefa ƙwallayen a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea.
Shima Vardy a jiya ya buga wasanni 212 inda ya jefa adadin ƙwallayen da Drogba ya jefa wato guda 104 kenan, da alama Vardy zai jefa kwatankwacin ƙwallayen da ya jefa a kakar wasan data gabata.
Daga wasan makon farko da aka fafata ayanzu haka Leicester City tana matsayi na 2 da maki 3 inda Arsenal ne a matsayi na 1 ahalin yanzu bayan sun lallasa Fulham daci 3 da nema tun a ranar Asabar.