Jami’iyyar APC ta samu nasarar lashe kujerun shuwagabannin ƙananan hukumomi, inda ta samu nasarar lashe kujeru 17, da Kansiloli na ƙananan hukumomin Jahar.
Jami’in Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta na Jahar Fabian Ntung ya sanar da sakamakon zaɓen a ranar Lahadi a Jos.
Me Ntung ya bayyana cewar Jami’iyyar APC ta lashe dukkanin kujeru 325 na Kansiloli a ƙananan hukumomi 17 na jahar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan sanda sun kama Mutane da ake zargin Yan kungiyar Asiri
Mr Ntung ya yabawa masu kaɗa ƙuri’un da suka tabbatar dacewa an yishi cikin gaskiya da kwanciyar hankali.
Hukumar dai ta hana Babbar Jami’iyyar Hamayya ta PDP daga shiga zaɓen, sakamakon wasu rikice-rikice na cikin gida.
Haka zalika, Jami’iyyar ta ƙalubalanci cire ta da aka yi a Babbar Kotu da Kotun Ɗaukaka ƙara, amma dukkanin su ta rasa yin galaba akan ƙarar.