Kwamitin Ruko na Jami’iyyar APC na Kasa, a ranar Talata ta nada Kwamitin sasanci na Jami’iyyar na Kasa.
Mambobin Kwamitin sun hada da; tsohon Gwamnan Jahar Nasarawa Sanata Abdullahi Adamu, da Ministan Ayyuka na Musamman George Akume, da tsohon Gwamnan Jahar Enugu Sullivan Chime, da sauran su.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Jami’iyyar na Kasa John Akpanudoedehe ya fitar a Abuja, inda yace Jami’iyyar ta nada Adamu, da Akume, da Dogara, da Chime, da Adebule, da sauran su a matsayin Kwamitin sasanci na Jami’iyyar na Kasa.
Sanarwar tace ” Shugaban Kwamitin Ruko na Jami’iyyar na Kasa Mai Mala Buni ya amince da nada Kwamitin sasanci na Kasa da suka hada da;
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutane goma sun mutu sanadiyar hadarin mota a kano
“Sanata Abdullahi Adamu a matsayin shugaba, da Otunba Moses Alake Adeyemo a matsayin Sakataren Kwamitin, da Sanata George Akume, da Sullivan Chime, da Ali Saad Birnin Kudu, da Yakubu Dogara, da Alhaji Suleiman Argungu, da Mrs Olurati I. Adebule da Dr. Mrs. Beta Edu.
Haka Zalika, za’a sanar da ranar kaddamar da mambobin Kwamitin sasancin.
A wani labarin kuma
Shugaban Kwamitin Majalisar Dokoki ta Kasa akan hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi Francis Ottah yace zai gabatar da wani kudiri dazai sanya Hukumar yaki da shan miyagun kwayoyi ta rika yin gwajin Kwaya lokaci zuwa lokaci, ga duk Wanda ke neman kujerar siyasa a Najeriya.
A cewar sa kudirin zai Kuma baiwa Hukumar damar gudanar da gwajin kwaya ga Jami’an tsaro, gami da Daliban dake neman guraben karatu a Manyan Makarantun Najeriya ya zama dole sai anyi masu gwajin Kwaya.
Dan Majalisar a jawabin daya fitar a ranar Litinin a tabakin mai taimaka masa akan Kafafen Yada Labaru Andrew Agbese, yace illolin kamuwa da cutar Shan miyagun kwayoyi ya fantsama a dukkanin bangarori na Al’umma, kuma gwajin Kwaya ne kadai zai iya wayarwa mutane Kai akan matsalar dake tattare da shan miyagun kwayoyin.
Ya bayyana cewa, yadda wasu Yan siyasa ke canja halayyar su gami da yawaitar ayyukan ta’addanci da ake yi a cikin Al’umma dukkanin su kwaya ce ta haifar su.
Ya jaddada cewa, za’a iya magance hakan idan ya zaman to wadanda suke fama da matsalar basa cikin masu Shan miyagun kwayoyi.
“Ina gabatar da kudiri dazai baiwa Hukumar Hana Shan miyagun kwayoyi ta Kasa, damar gudanar da gwaji ga dukkanin yan siyasa, da manyan ma’aikatan gwamnati, da Sojoji da sauran Hukumomin tsaro, gami da Matasa masu neman guraben karatu a Manyan Makarantun Kasa. Wannan zai kawo karshen hauka da ake yi a bangarorin gami da wayar wa Al’umma kai.
“Shan miyagun kwayoyi abune wanda ya mamaye ko’ina a cikin Al’umma, daga Makarantun Sakandire zuwa Jami’o’i, daga Arewa zuwa kudu, daga Yan siyasa zuwa Ma’aikatan Gwamnati. A takaice Najeriya itace kasa data fi kowace yawan masu Shan miyagun kwayoyi, kuma Tabar wiwi ita tafi yawaita a Kasar,”inji shi.