Tsohon mai magana da yawun Shugaban Kasa Doyin Okupe ya gargadi Shuwagabancin Jami’iyyar PDP akan sake tsaida Dan takarar Shugaban Kasa daga yankin Arewa a zabe Mai zuwa na Shekarar 2023, Yana mai cewa hakan zai iya sanyawa ta sake rasa kujerar ta.
Ya bayyana haka a lokacin da yake tattaunawa da yan Jarida a ranar Asabar a Abuja.
Okupe ya bayyana cewa, Shirin da Jami’iyyar PDP ta yi na tsaida Dan takara daga Kudu a zaben Shugaban Kasa na Shekarar 2019, shine ya kawo cikas a nasarar Jami’iyyar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kungiyar Dillalan Man Fetur ta janye yajin aikin da take yi a Jahohin Enugu, Ebonyi da Anambra
kara dacewa, har yanzu wasu mutane daga Jami’iyyar na yunkurin kawo Dan takara daga yankin Arewa a zaben Shekarar 2023.
Ya ce manyan yan siyasa na fita daga Jami’iyyar, a dalilin Shirin gabatar da Dantakara daga yankin Arewa.
Ya bayyana tsoron cewa, Jami’iyyar zata iya sake faduwa kafin Shekarar 2023, idan har canja Sheka ya cigaba da wakana.
Okupe ya kara dacewa, “matsalar canja sheka da ake samu a Jami’iyyar PDP baya da alaka ko kadan da rikice-rikicen dake faruwa a Jami’iyyar. Wannan dama yana faruwa ne a duk lokacin da aka tunkari Babban zabe a cikin Kasa.
“Duk Wanda suka fita daga Jami’iyyar suna da wata matsala da Shuwagabancin Jami’iyyar, musamman ta fuskar bangarantar da takara.
“Matsalar bangarantar da takara a Jami’iyyar bai kamata ace, ya zama abunda zai sanya a rika futa, domin an nada Kwamiti dazai lura da wannan matsalar, kuma nan bada jimawa ba zai kammala aikin sa, gami da gabatar da bincike da yayi.
“Bangarantar da takarar da Jami’iyyar PDP ta fara tun Shekarar 1998, ya faru ne a dalilin hasashen da Jami’iyyar tayi na kasancewa a saman mulki, amma daga lokacin data rasa ikon mulki a Shekarar 2015, komai sai ya canja gaba daya, Kuma dole a yi dubi akan wannan cigaba da aka samu.