Ministan ya ce jami’o’i masu zaman kansu guda 78 sun bayyana wa gwamnati cewa a shirye suke su ci gaba da darussa amma manyan makarantun gwamnati ba su cimma matsaya ba har yanzu. Ya bayyana fata da cewa; nan ba da jimawa ba za a samu sanar da ranar buɗe makarantun, amma ba sakaka ba sai da dokoki.
Ya kuma jaddada cewa babu ranar buɗe makarantu a Nijeriya. Sai dai ana kan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkar ilimi domin ganin yadda za a sake buɗe makarantun.
Minista a ma’aikatar Ilimi, Nwachukwu Nwajiuba ne ya bayyana hakan a yayin jawabin da ya yi a taron kwamitin yaƙi da Korona na ƙasa a birnin tarayya Abuja, inda ya buƙaci manyan makarantu da ke gunagunin ci gaba da rufe su da su ƙara haƙuri, tare da jan hankulan dalibai masu zanga-zanga a kan su daina zanga-zangar, da zarar lokacin bude makarantun ya yi, za a bude su.
Ya ƙara da cewa Ministan Ilimi, Adamu Adamu da kansa ya tattauna da masu ruwa da tsaki na manyan makarantu game da batun na sake buɗe su.
Nwajiuba ya ce bayan sauraron dukkanin ɓangarorin da abun ya shafa, zai tuntunbi kwamitin yaki da cutar na ƙasa domin yin nazari kafin a kai ga ayyana ranar buɗe makarantun.