Faransa ta kaddamar da gagrumin aikin wayar da kan daliban Nijeriya da zummar gayyato su domin neman ilimi a jami’o’in da ke sassan kasar ta Faransa.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen Turai ke ci gaba da bullo da tsare-tsaren takaita kwararar baki.
Darektar Tsangayar Kula da Harkokin Ilimin Jami’o’in Faransa a Nijeriya, Charline Fouchet ta shaida wa RFI hausa cewa harshen Faransaci ba zai hana daliban Nijeriya karatu a Faransan ba.
A cewar Fouchet, a halin yanzu akwai fannonin ilimi dubu 1 da 500 da ake koyar da su a harshen Turancin Ingilishi, kuma babu bukatar daliban su kware a harshen Faransanci kafin samun guraben karatu a Faransa
“Mun yi amanna cewa, dama ce gagaruma a je Faransa saboda mutum zai iya neman iliminsa a harshen Turanci ba tare da fuskntar turjiyar yare ba.” In ji Fouchet