Daga: Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ya bayyana jami’o’i mallakin gwamnatocin jihohi a matsayin marasa amfani.
Farfesa Osodeke, wanda ya bayyana a gidan Talabijin na Arise a safiyar Juma’a, yana mayar da martani ne kan kudurin da wasu jami’o’in jihohi suka dauka na janye yajin aikin da kuma komawa karatu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Atiku Ya Gargadi Mambobin Jam’iyyar Su Kan Kalaman Da Ke Kawo Cikas Ga Hadin Kan PDP
Ya ce ya kamata a tattauna a kan jami’o’in tarayya, kamar Jami’ar Nijeriya, Nsukka, UNN; Jami’ar Ibadan, Jami’ar Maiduguri, Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, da sauran su, wadanda a cewarsa su ne ainihin jami’o’in kasar nan.
Farfesan ya dage cewa duk sauran jami’o’in ba su taba shiga kungiyar ta ASUU ba kuma ba a lissafta su cikin wadanda suke yajin aiki ba.
“Jihar Yobe, ku je ku duba, kamar jami’ar jihar Kaduna, me ke faruwa a can? Don Allah kar a saita waɗannan misalan, ba su da mahimmanci.”
“Muna maganar, shin Ibadan na yajin aiki? UNN tana yajin aiki? ABU na yajin aiki? BUK tana yajin aiki? Maiduguri da Lagos suna yajin aiki?”
“Ina magana game da muhimman jami’o’i ba wadanda suke marasa amfani ba. Ba sa cikin yajin aikin mu. Kafa wadanda suke yajin aikin namu,” inji shi.
Kungiyar ASUU ta shiga yajin aikin ne tun ranar 14 ga watan Fabrairun bana, saboda inganta walwala, da farfado da jami’o’in gwamnati da dai sauransu.
Daya daga cikin batutuwan da malaman jami’o’in ke tabowa, shi ne rashin biyan kudaden farfado da jami’o’in, wanda ya kai kimanin Naira tiriliyan 1.1, domin duk kokarin da gwamnati ta yi na ganin kungiyar ta kawo karshen yajin aikin ya ci tura.
Gwamnati ta ce ba ta da kudin da za ta biya bukatun malamai.
A wani labarin kuma Gwamnan APC Ya Rage Wa Sarakunan Jiharsa Karfin Iko
Gwamnan jihar Ondo Oluwarotimi Akeredolu ya rage karfin ikon wasu sarakuna ta hanyar daukaka wasu Obas zuwa manyan sarakunan gargajiya.
Gwamnan wanda ya hana rufe kasuwanni saboda bukukuwan gargajiyar ba tare da amincewar sa ba, ya kuma daukaka wasu sarakuna zuwa matsayin Obas a cikin al’ummar jihar.