Gabanin babban taron da za a yi a ranar 26 ga watan Fabrairu, jam’iyyar APC Mai Mulki ta musanta raba mukaman jam’iyyar na shiyya.
Sakataren kwamitin rikon kwarya na kwamitin tsare-tsare na kasa (CECPC), Sanata James Akpanudoedehe ne ya bayyana hakan, yayin da yake ganawa da manema labarai ranar Laraba a Abuja, ya ce kwamitin bai dauki matsaya ba kan raba mukaman shiyya-shiyya.
Ya bayyana rahoton da wasu kafafen yada labarai suka yi cewa an ware mukaman jam’iyya daban-daban, karya ne.
Sakataren ya ce, “Mu ma mun zo ne domin mu yi watsi da labaran karya da ke yawo a kafafen sada zumunta na zamani cewa mun ware ofisoshin jam’iyya, har yanzu ba mu amince a kan batun shiyya-shiyya ba.
Sai dai a wata sanarwa da Akpanudoedehe ya sanyawa hannu a karshen taron jam’iyyar karo na 19 a ranar Laraba, ya ce sun yi la’akari da kuma aiwatar da jaddawalin ayyukan da za’a gudanar a taron.
Ya ce za a fara sayar da fom ga duk masu neman mukaman a kasa a ranar 14 ga Fabrairu.